1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fafaroma ya yi tur da ayyukan 'yan ta'adda a yankin Sahel

May 10, 2026

A Chadi Boko Haram ta halaka sojoji 26, har ma kasar ta ayyana dokar ta-baci, tare da rufe iyakokinta, haka ma a Mali.

https://p.dw.com/p/5DY6C
Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Leo na 14
Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Leo na 14Hoto: Stefano Costantino/TTL/Avalon/Photoshot/picture alliance

Jagoran kirsitoci mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Leo na 14, ya yi allawadai da hare-haren da aka kai kasashen yankin Sahel, musamman na Mali da Chadi kwanan nan, wanda 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi suka kashe jama'a da dama.

Karin bayani: Mali ta ce ba za ta tattauna da kungiyoyin ta'adda ba

Fafaroma Leo ya yi wannan jawabi ne, yayin addu'o'in da ya jagoranta yau Lahadi a dandalin St Peter's na fadarsa ta Vatican, inda ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan, tare da fatan ganin karshen wannan masifa, domin samun dawwamammen zaman lafiya da ci gaban rayuwar jama'a.

Karin bayani:An sanya dokar ta baci a Tafkin Chadi 

Ko a ranar Asabar an samu rahoton kisan da kungiyar JNIM, mai alaka da Al-Qaeda ta yi wa mutane 30, a kasar Mali ranar Laraba, bayan far wa kauyukansu.

Karin bayani: Fafaroma Leo ya yi kiran a yi adalci a nahiyar Afirka

Yayin da a Chadi ma 'yan Boko Haram suka halaka sojoji 26, har ma gwamnatin mulkin sojin kasar ta ayyana dokar ta-baci, ta tsawon kwanaki 20, tare da rufe iyakokinta, a kokarinta na yi wa 'yan ta'addar kofar rago.