Kara tura 'yan sandan Kenya zuwa Haiti
December 9, 2025
Kenya ta kara turo daruruwan 'yan sandan kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Haiti, sakamakon matakin fadada rundunar ta kasashen duniya. Kungiyoyi masu dauke da makamai sun tarwatsa lamura a kasra ta Haiti, abin da ya tilasta wa Firaminista Ariel Henry ajiye aiki a farkon shekara ta 2024.
Matsalolin tsaron Haiti
Wani kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kimanin kaso 90 cikin 100 na birnin Port-au-Prince fadar gwamnatin Haiti na hannun kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda suka yi kaurin suna wajen kisa, da fyade, da kwashe duniyar jama'a gami da garkuwa da mutane.
Kenya dai ta tura karin dakaru 'yan sanda 230 daga cikin matakan na neman daidaita lamura a kasar ta Haiti, an dai shirya zabukan kasar na shugaban kasa da 'yan majalisa a shekara mai zuwa ta 2026