1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tasirin tura dakarun Chadi zuwa Haiti?

Mouhamadou Awal Balarabe Blaise Dariustone/SB
March 31, 2026

Chadi ta yi alkawarin tura jami'an 'yan sanda da jandarmomi zuwa Haiti don yaki da kungiyoyin asiri da na daba. Amma mene ne fa'idar da Chadi za ta samu idan ta shiga Haiti, kuma wane hadari ne sojojinta za su fuskanta?

https://p.dw.com/p/5BRFq
Shugaba Mahamat Idriss Deby na Chadi tare da sojojin kasar
Shugaba Mahamat Idriss Deby na Chadi tare da sojojin kasarHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Wadannan jami'an tsaron Chadi za su kasance cikin sabuwar rundunar da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a watan Satumban da ya gabata. Amma mene ne fa'idar da Chadi za ta samu idan ta shiga Haiti, kuma wane hadari ne sojojinta za su fuskanta?

Tasirin tura dakarun

Sojojin kasar Chadi
Sojojin kasar ChadiHoto: Ali Kaya/AFP/Getty Images

Jimillar jami'an 'yan sanda da jandarmomi da sojoji 750 ne Chadi za ta tura kasar Haiti tun daga watan Afirulun 2026 don taimakawa wajen yakar kungiyoyi da ke aikata ta'asa da makamai da suke dauke da su.

Wannan yunkuri na fadar mulki ta Ndjamena, wani bangare ne na aikin kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ke tallafawa kuma, wanda aka dora masa alhaki karkashin wata runduna na dawo da tsaro a Port-au-Prince, inda kungiyoyin 'yan daba suka karbe iko da kusan duk sassan babban birnin kasar Haiti.

Masanin kimiyyar siyasa na Chadi Evariste Ngarlem Toldé, ya ce shiga cikin wannan aiki na inganta tsaron Haiti da Chadi ta yi na ba da fa'idodi da dama ga kasar domin wannan tura jami'an tsaro yana bai wa sojojin Chadi horo mai zurfi da kwarewar aiki ta musamman a cikin wannan yanayi mai sarkakiya. Kazlika yana bai wa Chadi damar samun kudade daga Majalisar Dinkin Duniya da kayan aiki, kuma a karshe, yana bai wa gwamnatin Chadi damar karfafa tasirin diflomasiyya.

Aikin dakarun a Haiti

Sojojin kasar Chadi
Sojojin kasar ChadiHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Ana sa ran wannan rundunar da ake wa lakabi da FRG , wacce za ta hada da sojojin Chadi, za ta maye gurbin wani aikin tsaro na kasashen duniya wanda Kenya ke jagoranta tun watan Yunin 2024, amma ba ta samu ci gaban a zo a gani ba a yaki da kungiyoyin masu aikata laifuka a birnin Port au Prince. Sai dai mai sharhi kan siyasa na Chadi Yamingué Betinbaye, ya ce wannan aiki ne mai hadari sosai.

Wasu masu lura da al'amuran da ke je ya zo na ganin cewar ya kamata hukumomin Chadi su fi mai da hankali kan tsaron cikin gida da kasar da ke fama da shi musamman ma rikice-rikice tsakanin kabilu.

Sannan kuma Ndjamena ta tabbatar da tsaro a kan iyakarta da Sudan, inda hare-haren a tsakanin 'yan Sudan da ba sa ga maciji da juna suka karu a cikin 'yan kwanakin nan, lamarin da ya haifar da mutuwar mutane da yawa a bangaren Chadi.