1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada sabon sarkin Dutse da ke Jaigawa

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
February 5, 2023

Hukumomi a jihar Jigawa sun yi nadin sabon sarkin Dutse kwanaki bayan rasuwar tsohon sarkin Dutse Nuhu Muhammad Sunusi. Hamim Muhammad Nuhu Sunusi ne ya zama sarki na 19 na daular Fulani a masarautar Dutse.

https://p.dw.com/p/4N7a5
Tutar NajeriyaHoto: Leonid Altman/Zoonar/picture alliance

Kwanaki biyar bayan rasuwar Sarkin Dutse mai martaba Nuhu Muhammad Sunusi, gwamnan Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya amince da nadin Hamim Muhammad Nuhu Sunusi da ga marigayin a matsayin sabon sarki Dutse a jihar Jigawa, kamar yadda wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta tabbatar wa wakiliyarmu a Jigawa Zainab Shu'aibu Rabo.

Hameem mai shekaru 42 a duniya, zai kasance sarki na 19 a jerin sarakunan Fulani kuma sarki mai daraja ta 1 a jihar Jigawa. Ya samu rinjayen kuri'un wadanda suke zaban sarki kafin gwamnan jihar Jagawa ya tabbatar da nadin sabon sarkin