1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin wadanda suka mutu a ambaliyar Mexico na karuwa

October 20, 2025

Adadin wadanda suka mutu sun haura 76 a Mexico, sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar kasa.

https://p.dw.com/p/52JNg
Yadda ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Mexico
Yadda ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a MexicoHoto: Hector Quintanar/AFP

Kimanin kauyuka 119 ne ambaliyar ruwan ta shafa, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi ta shatatawa na tsawon kwanaki, kamar yadda wani sabaon rahoton da aka fitar ya tabbatar.

Tuni ma hukumomi suka sanar da cewa suna ci gaba da kai kayyakin jin-kai ga mabukata da bala'In ya shafa, inda ake shigar musu da kayan abinci da magunguna da tufafin sawa.

Jihar Hidalgo da ke makwaftaka da babban birnin Mexico ce jihar ta fi shafa kai tsaye, inda kananan hukumomi 65 da galibi suke cikin tsaunika ne suka fi fadawa cikin taraddadi in ji hukumomin agaji.