Afirka ta Kudu ba za ta halarci G20 na 2026
December 4, 2025
Talla
Kakakin shugaban Afirka ta Kudu Vincent Magwenya ya ce Pretoria za ta janye daga jerin tarurrukan na G20 na shekara ta 2026.
Kuma za ta ci gaba da shiga lokacin da aka mika wa Birtaniya ragamar gudanar da taro a shekara ta 2027.Dangantaka tsakanin Washington da Pretoria ta sukurkurce tun bayan da Donald Trump ya sake koma Fadar White House.
Washington na zargin Afirka ta Kudu da tursasawa Afrekaner wani bangaran al ummar kasar 'yan asalin Turai na farko a Afirka ta Kudun , abin da pretoria ta musunta.