1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Amurka da EU sun kakabawa kamfanonin man Rasha takunkumai

October 23, 2025

Kwanaki biyu bayan sanar da dakatar ganawar da ake sa ran yi a tsakanin Trump da Putin, Amurka da EU sun kakabawa manyan kamfaonin man Rasha takunkumai a matsayin matsin lamba.

https://p.dw.com/p/52S82
Matatar man fetur ta Tuapse da ke Rasha
Matatar man fetur ta Tuapse da ke RashaHoto: Igor Onuchin/imago images/ITAR-TASS

Gwmanatin Amurka ta sanar da kakaba takunkumai kan wasu manyan kamfanonin mai na kasar Rasha, kwanaki biyu bayan kawar da yuwuwar sake ganawa a tsakanin Trump da Putin kan batun kawon karshen yakin Ukraine.

Karin bayani: An dakatar da ganawar Trump da Putin

A lokacin da yake sanar da wannan mataki a gaban sakataren NATO Mark Rutte a fadar White House, shugaba Donald Trump ya ce yana fatan nan ba da jimawa ba wannan matsin lamaba zai yi tasiri kan Moscow domin amincewa ta dakatar da yakin a Ukraine.

A daya gefe kuma kungiyar Tarayyar Turai ita ma ta sanar da cimma matsaya kan kara tsaurara takunkumai kan kamfononin man Rasha, da nufin raunana hanyoyin da Moscow ke samu kudaden shiga domin ci gaba da daukar nauyin yakin da take yi a Ukraine.

Wannan sanarwa ta karin takunkumai ga kamfanonin man Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Moscow suka kaddamar da wani gagarumin hari da jirage maras matuka akalla 400 da kuma makamai masu linzami a sassa daban-daban na Ukraine, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane shida.