Amurka ta ce Rasha na da niyyar katse yakin Ukraine
December 4, 2025
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya ce yana ganin Shugaba Putin na Rasha na da aniyar kawo karshen yakin Ukraine, duk da cewa tattaunawar da wakilan Amurka suka yi a Moscow ba ta samar da matsaya ba.
Mr. Trump ya bayyana hakan ne yayin da ake shirin wani zagayen tattaunawa da babban wakilin Ukraine a game da neman tsagaita wuta.
Shugaban na Amurka ya kara da cewa wakilansa Steve Witkoff da Jared Kushner sun ji alamar cewa Putin na son a kawo karshen rikicin, kuma ya tabbatar da cewa Ukraine ta amince da shirin zaman lafiya da Amurka ta tsara.
Sai dai duk da doguwar tattaunawar da aka yi, ba a kai ga cimma matsaya ba, kuma Fadar Kremlin ta ce ba ta yarda da wasu sassa na shirin ba, ciki har da batun Ukraine ta mika wasu yankunan Donbas da har yanzu take rike da su, shekaru hudu bayan mamayar Rasha.