1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta umurci kwashe 'yan kasarta daga Abuja

Uwais Abubakar Idris ZMA
April 9, 2026

Gwamnatin Amurka ta bada umurnin a kwashe ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke Abuja hediwatar Najeriya saboda abinda ta bayyana da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.

https://p.dw.com/p/5Bvuz
Nigeria US-Botschaft in Abuja
Hoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Lamarin ya sanya maida martani da duba tasirin da wannan zai yi ga yadda ake kallon Najeriyar a kasashen waje. Kasa da sao'i 24 bayan da kungiyoyin farar hula 52 suka bayyana damuwarsu a kan halin rashin tsaro a Najeriyar ne gwamnatin Amurikan ta fitar da wannan bayani a matsayin shawarar da takan baiwa ‘yan kasarta da ke zaune a Najeriya.

Kaiwa ga wannan mataki na bada umurnin a kwashe ma'aikatan ofishin jakadancin nata wadanda aikinsu bai zama dole ba bisa dalilai na tsaro ya sanya daukar hankali, musamman sanin yadda ake kallon Abuja a matsayin hedikwtar Najeriyar da ke samun kulawa ta tsaro sosai.

Nigeria Abuja 2025 | Präsident Bola Ahmed Tinubu hält Ansprache zum Unabhängigkeitstag
Hoto: Nigerian Presidency/Handout/Anadolu/picture alliance

A baya dai Amurkan kan fitar da bayanai na shawara da jan hankali ne ga ‘yan kasarta a kan inda ya kamata su yi takatsantsan na tafiye-tafiye. Allah milsali a ‘yan shekarun nan ta sha jan kunnen yan kasar nata su guji tafiye-tafiye zuwa yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar da ake fama da ayyukan ta'adanci da ma wasu sassan da ake fuskantar garkuwa da jama'a kama daga arewa da ma kudancin kasar, kaiwa ga sanya Abuja a lamarin ya sanya jefa ayar tambaya. Amma ga Farfesa Ghali Sherrif da ke zama kwararre a fanin dimplomasiyyar kasa da kasa da ke jami'ar Abuja, ya ce akwai dai dalilan daukar wannan mataki.

An dai ga karuwa na bada irin wannan shawara daga Amurka ga 'yan kasarta tun bayan yarjejeniyar da ta cimawa da Najeriyar a fanin tsaro da ya bata ikon kai hari kai tsaye a kasar. Gwamnatin Najeriyar dai ta sha nanata cewa tana iyakar kokarinta wajen kyautata yanayin tsaro a kasar kamar yadda ministan yada labaru da wayar da kan jama'a Mohammed Idris ya bayyana. Duk da karuwar kai hare-hare da ake ganin a ‘yan makwanin nan wannan bai kaiga shafar Abuja hedikwatar kasar ba.