1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta ce ISIS na kara shiga Afirka ta Yamma

May 12, 2026

Wani sabon rahoton tsaron Amurka ya yi gargadin cewa kungiyar ISIS na kara yada tasirinta zuwa yankin Sahel da wasu sassan yammacin Afirka, lamarin da ke kara tayar da hankula kan makomar tsaro a yankin.

https://p.dw.com/p/5Df07
wasu 'yan ta'adda masu alaka da ISIS a Afirka
wasu 'yan ta'adda masu alaka da ISIS a AfirkaHoto: Feisal Omar/REUTERS

Wani sabon rahoton tsaro daga Amurka ya yi gargadin cewa kungiyar ISIS na kara yada tasirinta zuwa nahiyar Afirka, musamman yankin Sahel, Tafkin Chadi da wasu kasashen yammacin Afirka, lamarin da ke kara barazana ga tsaron yankin.

Rahoton ya ce raunin tsarin mulki da talauci da rashin aikin yi da ma matsalolin tsaro a kasashen yankin na daga cikin abubuwan da ke bai wa kungiyar damar samun gindin zama da kuma jawo samun sabbin mayaka.

Haka kuma, janyewar sojojin kasashen yamma daga wasu yankuna kamar Nijar ya haifar da gibin tsaro da kungiyoyin masu dauke da makamai ke amfani da shi wajen fadada ayyukansu.

Irak | Soldat in Baghdad (Archiv)
Hoto: Ameer Al Mohammedaw/dpa/picture alliance

Rahoton ya ce akwai yiwuwar kungiyoyin da ke da alaka da ISIS su kara bazuwa zuwa kasashen gabar teku irin su Togo da Benin da kasar Ivory Coast.

A Najeriya ma, ana ci gaba da ganin alamun karuwar ayyukan kungiyar a wasu sassan arewa maso yamma da kuma tsakiyar kasar, inda hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula suka sake karuwa.

A cikin wannan makon ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon mashawarcin tsaron cikin gida domin karfafa yaki da matsalar rashin tsaro da ta'addanci da kasar ke fuskanta.

Masana tsaro sun ce ci gaba da karuwar tasirin ISIS a yankin Sahel na iya mayar da wasu kasashen Afirka fagen fafatawa tsakanin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da manyan kasashen duniya, musamman yayin da rikice-rikice da talauci ke kara tsananta a yankin.