Amurka za ta fara rakiyar jiragen ruwa a Hormuz
May 4, 2026
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce kasarsa za ta kaddamar da aikin ba da da kariya da rakiya ga jiragen ruwa na 'yan kasuwa da ke wucewa ta mashigin Hormuz, sakamakon korafin da wasu jirage suka yi cewa an kai musu farmaki da makamai.
Karin bayani: Trump ya ce ba tabbas za a amince da shawarar Iran
Mr Trump ya yi wa aikin lakabin Project Freedom, wanda zai fara a wannan Litinin, inda zai aike da jami'ai 20,000 da suka kware wajen aiki da jiragen ruwa, domin rage cunkoson daruruwan jiragen da suka yi jerin gwano a gabar ruwan.
Karin bayani: Putin ya yi waya da Trump kan yakin Iran
To sai dai Iran ta kira wannan mataki a matsayin keta yarjejeniyar tsagaitar wutar yaki da suka cimma, tare da haifar da rudani, kamar yadda shugaban majalisar shawara kan sha'anin tsaro ta kasar Ebrahim Azizi ya wallafa a shafinsa na X.
Karin bayani:Amurka ta janye sojinta daga Jamus bayan kin yakin Iran
Amma babu wani karin bayani daga shelkwatar tsaro ta Amurka Pentagon kan yadda aikin zai kasance ba, wanda ke faruwa sa'o'i kalilan bayan da Iran ta ce tana nazartar martani da shugaba Trump ya yi wa tayin da ta mika masa, na kawo kawo karshen yakin da kasashen biyu suke gwabzawa.