An sace wasu mutanen a Jihar Kwaran Najeriya
November 25, 2025
Talla
Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kwara Adekimi Ojo ya shaida cewar wasu mutanen dauke da makamai sun yi harbi sama
kafin su yi awan gaba da mutanen goma a kauyen Isapa, wanda ya ce galibin wadanda aka sacen manoma ne da yara .
Wannan satar mutane na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙasar da ta fi yawan jama'a a Afirkake fuskantar sabon salon garkuwa da mutane.
Makon da ya gabata, an yi garkuwa da masu ibada 35 a lokacin wani hari da aka kai wa wata coci mai nisan kilomita 20 daga Isapa, a ƙauyen Eruku.