1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi jana'izar tsohon firaministan kasar Kenya Raila Odinga

Binta Aliyu Zurmi
October 19, 2025

An gudanar da jana'izar madugun adawar kasar Kenya Raila Odinga, bayan shafe kwanaki ana gudanar da bukukuwan tunawa da irin gudumawarsa a fagen siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/52FQm
Kenia Bondo 2025 | Militärische Ehrenwache bei Raila Odingas Beerdigung
Hoto: Luis Tato/AFP

Odinga ya mutu yana da shekaru 80 a duniya. Dan siyasar ya kwashe shekaru yana fafutukar tabbatar da dimukuradiyya a lokacin mulkin kama-karya na Daniel arap Moi fafutukar da ta kai shi gidan yari da gudun hijira.

Dubban mutane ne suka yi dafifi a mahaifarsa da ke birnin Bondo a yammacin kasar, domin jana'izar. Al'ummar kasar da dama sun bayyana cewar, an yi rashi kuma ba za su manata da irin gudumawar da ya bayar ga kasarsa ba.

Za a iya cewa shi ne dan siyasa mafi karfi a zamaninsa a Kenya, domin Odinga ya rike mukamin firaminista daga shekara ta 2008 zuwa 2013 amma bai taba samun nasarar lashe zaben shugaban kasa ba duk da yunkurin da ya yi har sau biyar.

Karin Bayani:Turmutsutsi wajen karrama gawar Odinga