An yi yunkurin cafke wani 'dan fafutukar Tanzaniya a Nairobi
February 24, 2026
Dan fafutukar mai suna Mshabaha Mshabaha Hamza, na daya daga cikin mutanen da suka yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Tanzaniya, kan yadda ta yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe masu zanga-zanga, a lokacin da aka gudanar da babban zaben kasar. Mutane sama da 2,000 suka mutu a yayin zanga-zangar. Ana dai zargin gwamnatin Tanzaniya da kin fitar da rahoton ta'asar da aka yi a yayin boren.
Karin bayani:Amnesty ta zargi Tanzania da batar da gawarwakin 'yan adawa
A shekarar 2024, an sace madugun adawar Uganda Kizza Besigye a birnin Nairabi, inda aka gurfanar da shi a kotun Kampala kan zargin cin amanar kasa. Kazalika a watan Janairun 2025, an sace wata lauya mai fafutukar kare hakkin bil Adama, Maria Sarungi Tsehai, a birnin Nairobi, to amma daga bisani ta shaki iskar 'yanci bayan kwarmaton da manema labarai da kuma kungiyoyin kare hakkin bila Adama suka yi na labarin cafke ta.