Azumin Musulmi ya zo lokaci guda da Lent na Kirista
February 18, 2026
Watan azumin Ramadana ya kasance lokacin da al'umma ke kara kusantar da kansu ga ubangiji don samun ceto da rahamarsa. A ranar Laraba 18.02.2026 ne al'ummar Musulmi suka fara Azumin Ramadana da kan iya kai kwanaki 29 ko 30.
Su ma mabiya addinin Kirista sun fara azumin Lent, Inda sukan shafe kwanaki 40 suna gudanar da shi. Rev. Auta Yohana, mataimakin magatakardar mujami'ar COCIN Jos Jarawa a jihar Filato ya ce manufar yin Azumin Lent ga mabiya addinin kirista shi ne: "don tunawa da lokacin da Yesu ya mutu har ya tashi daga kabari... Ana kuma tuna rayuwa don ba har abada aka zo ba. Sannan ana sadaka da taimaka wa gajiyayyu da karfinsu bai kai ba."
Bambancin azumin Ramadana da Lent
A bangare guda, malaman addinin Musulunci na yin amfani da azumi wajen fadakar da al'ummar Musulmi fa'idar da ke tattare da watan Ramadana, musamman wajen kara fuskantar ayyukan ibada da kuma nisanta kai daga munanan ayyuka.
Karin bayani: Azumi: kamanceceniyar dabi'u tsakanin Kirista da Musulmi
Nazir Shazali Ali, daya daga cikin malaman Musulunci a garin Jos na jihar Filato ya ce akwai koyarwa ga Musulmi a cikin watan Ramadana. Ya ce: "Allah ya yi mana wannan domin mu kusance shi... Shi azumi an yi shi ga dukkanin al'umomi na annabawa tun daga kan annabi Nuhu."
A cikin azumin Ramadana, al'ummar Musulmi na zamantowa cikin ibada, tare da kame baki daga ci ko sha, tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana. Yayin da a gefe guda, mabiya addinin kirista kan kaurace wa wasu na'ukan abinci har na tsawon kwanaki 40 domin kyautata tsarki cikin zukatansu .
Kiraye-kirayen taimaka wa marasa karfi
Rev. Yakubu Pam, Shugaban kungiyar mabiya addinin kirista ta kasa reshen jihohin arewacin Najeriya ya yi nasiha ga mabiya addinan guda biyu. Ya ce: "Ubangiji ya ji tausayi, ya wanke mana duk kuskure da muka yi. Akwai ma wadanda za ka gan su a kan titi suna adu'a Allah ka taimake ni."
Karin bayani:Taimakon Azuni a Najeriya
Shugabanin daga bangaren addinan biyu na ci gaba da kiraye-kiraye wajen ganin cewar al'umma masu hannun baiwa sun taimaka wa gajiyayyu domin su samu saukin gudanar da ibada.