1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barayi sun kwashe kayayyaki a gidan tarihi a Paris

October 20, 2025

Kayayyakin tarihi da na kwalliya masu tsadar gaske ne wani gungun barayi ya yi awon gaba da su a birnin Paris na kasar Faransa, inda 'yan sanda ke neman su ruwa-a-jallo a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/52G3K
Gidan Apollon a Louvre na Paris inda barayi suka kwashe kayayyaki masu daraja
Gidan Apollon a Louvre na Paris inda barayi suka kwashe kayayyaki masu darajaHoto: Stephane de Sakutin/AFP

Wani gungun 'yan fashi sun yi nasarar sace kayan tarihi da na kwalliya masu tsadar gaske daga Gidan Tarihi na Louvre da ke birnin Paris na kasar Faransa.

Hukumar adana kayan tarihi a birnin na Paris ta sanar da rufewa na wani dan lokaci saboda halin gaggawa da aka tsinci kai a ciki.

Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Lahadi, da misalin karfe uku na asuba agogon Faransa, inda 'yan fashin suka kutsa cikin ginin da ke tsakiyar birnin na Paris, suka kwashe fitattun kayan fasaha da kayan ado masu daraja, kafin su tsere da babura.

Hukumar 'yan sanda ta ce tana ci gaba da neman su a ko'ina cikin Faransar.

Gidan Tarihi na Musée du Louvre shi ne mafi shahara a duniya, kuma yana jawo baki daga sassan duniya daban-daban, inda fitaccen zanen Mona Lisa ta Leonardo da Vinci ke daya daga cikin manyan abubuwan da suka fi daukar hankali a cikinsa.