1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Matakin dakile bakin haure a Birtaniya

Suleiman Babayo Naziru Mikail
November 18, 2025

Sabbin tsare-tsaren da gwamnatin Birtaniya ta sanar domin rage yawan masu neman mafaka da kuma ‘yan ci-rani da ke shiga kasar ba bisa ka'ida ba, na ci gaba da jan hanakalin jama'a da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

https://p.dw.com/p/53pdC
Bakin haure masu neman mafaka
Bakin haure masu neman mafakaHoto: Gareth Fuller/PA/AP/picture alliance

A wani mataki da masana suka ce shi ne mafi girma a shekaru masu yawa, Sakatariyar Harkokin cikin Gida Shabana Mahmood, ta bayyana cewa muhimman sauye-sauye domin dakile yawan masu shigar kasar ba bisa ka'ida ba.

Matakan da aka dauka

Bakin haure masu neman mafaka
Bakin haure masu neman mafakaHoto: Daniel Leal/AFP/Getty Images

Daga yanzu, za a rinka bai wa ‘yan gudun hijira izinin zama na wucin gadi ne kawai, inda za a rinka nazari kan matsayinsu duk bayan shekara biyu da rabi. Sannan sai mutum ya shafe shekara 20 kafin ya samu damar zaman a dindin a birtaniyar maimakon shekara biyar da ake yi a yanzu.

Ma'aikatar cikin gidan za ta kuma ta sauya yadda ake gudnar da shari'ar masu neman mafaka, inda za a takaita damar da suke da ita ta daukaka kara ta hanyar tilasta musu hade duk wata hujja da suke da ita wuri guda maimakon tsittsinkawar da ake yi a yanzu.

Hakazalika za a daina basu tallafin kudi na mako-mako da kuma muhalli. Sai dai za a samar da wasu sabbin hanyoyi kamar na aiki da karatu da za su iya bai wa ‘yan gudun hijira damar zaman a dindin a kasar.

Ana iya cimma burin?

Daya daga cikin bakin haure masu neman mafaka
Daya daga cikin bakin haure masu neman mafakaHoto: Niklas Halle'n/AFP/ Getty Images

Sannan duk kasashen da suka ki karbar ‘yan kasarsu, to za su fuskanci takunkumi da ya hada da na hanasu visar shiga Birtaniya.

Masana da dama na ganin gwamantin na daukar wannan mataki ne domin farfado da kimarta a idon ‘yan kasar – da kuma tagomashin da jam'iyyar masu kyamar baki ta Reforms UK ke kara samu.

To ko sabbin matakan za su taimaki jam'iyyar ta Labour, Dr Hamisu Hadeja malami ne a Jami'ar Warwick da ke Ingila yana ganin haka zai iya yin tasiri wajen shawo kan wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar Labour wadanda suka fara komawa Reforms.

Wani abu da ake ganin zai iya kawo cikas ga wadannan sauye-sauye shi ne yadda za a gabatar da su ga fannin shari'a, musamman dokokin da shuka shafi hakkin bil'adama da kuma kotun kare ‘yan cin dan adam ta Tarayyar Turai – wacce Birntaniya mamba ce a cikinta.