Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine ya kashe mutane 20
November 19, 2025
Talla
Sabbin hare-haren su ne mafi muni da aka kai a Ukraine tsawon makonni kuma daya daga cikin mafi muni a yammacin kasar tun bayan da Moscow ta fara mamaya a shekarar 2022.
Hotunan da jami'ai suka fitar sun nuna benaye da dama na wani katafaren gini da aka baje, inda ma'aikatan ceto ke bi ta tagogi da aka barke. Titunan birnin sun cika da tarkace kuma wasu sassan birnin sun cika da hayaki mai kauri bayan da aka samu rahotonfashewar abubuwa.
Masu aikin ceto sun ciro gawarwaki daga cikin guraguzan benayin da suka fado, yanzu haka dai harin na dasa ayar kan tasirin ziyarar Shugaba Zelensky a Turkiyya.