1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

DW ta soki Rasha kan sanya ta a matsayin wacce ba a bukata

Mouhamadou Awal Balarabe
December 15, 2025

Darakta Janar ta DW Barbara Massing DW ta mai da martani ga matakin Rasha na ayyana ta a matsayin kungiya ko ma’aikatar da ba a bukatar zamanta a kasar. DW ta ce babu abin da zai sauya a aikinta cikin ‘yancin a Ukraine.

https://p.dw.com/p/55NCv
Darakta Janar ta Deutsche Welle Barbara Massing
Darakta Janar ta Deutsche Welle Barbara MassingHoto: Stephanie Englert/DW Images

Ofishin babban mai gabatar da kara na Rasha ya ayyana gidan rediyon da talabijin na kasa da kasa na Jamus Deutsche Welle a matsayin "kafa ko kungiya da ba a so a kasar," bisa zargin zama jagora a farfagandar kin jinin Rasha.

Wannan mataki da majalisar dokokin Rasha (Duma) ta nema tun daga watan Agusta, ya sanya tashar DW a sahun wasu kafofin watsa labarai da dama da kungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyi da aka riga aka kafa wa karar tsana a kasar.

Karin bayani: Deutsche Welle: Shekaru 70 da kafuwa

A karkashin dokar Rasha dai, daga yanzu duk hadin gwiwa da wadannan kungiyoyi da kafofin watsa labarai na zama laifi bisa ga hukunci tara ko ma dauri a kurkuku. Haka kuma, ana daukar tura bidiyoyi da rahotannin da DW ke watsawa a matsayin laifi.

Darakta Janar na DW Barbara Massing ta ce matakin da hukumomin Rasha suka dauka, wata alama ce da ke nuna cewa Kremlin na nuna adawa da 'yancin fadar albarkacin baki a kasar. Massing ta kara da cewa yunkurin ya nuna yadda Rasha ta bayyana tsoronta ga 'yan kasarta da ke neman sahihan bayanai, da wadanda ke tunani mai zurfi.