EU ta sanya sojin Iran cikin 'yan ta'adda
January 29, 2026
Kamfanin dillancin labaran Jamus dpa ya ruwaito cewa ana kara samun nuna goyon baya don ayyana rundunar sojin juyin-juya halin Iran a matsain kungiyar 'yan ta'adda.
A karkashin takunkumin na kungiyar tarayyar Turai, an haramta tafiye-tafiye zuwa wasu kasashe ga jami'an kasar ta Iran tare da rike kadarorin kasar da na wasu daidaikun mutane.
Kungiyar tarayyar Turan ta ce nan ba da jimawa ba za ta wallafa sunayen mutanen da takunkumin ya shafa. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya ce wadanda takunkumin ya shafa sun hadar da jami'an gwamnati da masu gabatar da kara da kuma shugabannin wasu sassa na 'yan sandan kasar ta Iran.
Rahotanni sun ce an kashe mutane tsakanin 300-zuwa 1000 a dirar mikiyar da jami'an tsaro suka yi kan masu zanga-zangar da ta karade Iran baki daya.