Fafaroma Leo ya kadu da sace dalibai a Najeriya
November 23, 2025
Talla
Fafaroma Leo ya nuna matukar kaduwarsa game da sace-sacen malaman addinini da dalibai a kasashen Najeriya da Kamaru. Shugaban darikar Katolikan ya kuma bukaci jama'a da su yi wa yaran maza da mata da aka sace addu'a, tare da fatan mujami'u da kuma makarantu za su ci gaba da kasance wuraren da ke da tsaro.
Karin bayani: Wane hali iyayen dalibai ke ciki a Kebbi?
A ranar Litinin ce 'yan bindiga suka kai hari wata makarantar kwana ta mata a jihar Kebbi inda suka sace dalibai 25.Da safiyar ranar Juma'a suka sace wasu daliban a makarantar St Mary da ke jihar Neja. Har yanzu Najeriya na ci gaba da jimamin sace 'yan matan Chibok fiye da 300 da mayakan Boko Haram suka yi shekaru fiye da 10 da suka gabata, 'yan matan da har yanzu ba a ga wasu ba.