Masanan kimiyya sun lashe kyautar Nobel ta bana
October 7, 2025
Masanan kimiyya uku ciki har da dan kasar Burtaniya sun lashe kyautar Nobel ta fannin Ilmin Physics a wannan shekara bayan da kwamitin bayar da kyautar ya yaba da bincike mai zurfi na kimiya da suka gudanar kan wani fannin kimiyya na quantum.
Masu yaki da makaman nukiliya sun lashe lambar yabo ta Nobel
Masanan kimiyar da suka hada da John Clarke dan Burtaniya da Michel Devoret na Faransa da Ba Amurke John Martinis sun samu kyautar ce bayan gano yadda sinadarin quantum ke tantance makamashi a cikin tsarin lantarki a kimiyance, kamar yadda kwamitin bayar da kyautar ya sanar a wannan Talata
Makamanciyar kyautar Nobel 2023
Kwamitin ya ce hanyar da aka yi amfani da ita ta kasance muhimmiya wajen gano sidanaren dake bunkasa sabbin hanyoyi na kimiyyar kantarki.