Gagarumin matakin yaki da matsalar tsaro a Nijar
December 29, 2025
Matakin ya biyo bayan wasu take- take da ake gani na wasu manyan kasashe da ke yin biris da dokoki na kasa da kasa don neman cimma wata manufa tasu ko kuwa za su hada kasashe ko wasu kabilu su yaki juna ko tayar da zaune tsaye. Ta haka ne wannan mataki na Nijar ke kira ga hadin kan ya kasa don kariyar kasa daga ko wace kofa ta shigowa cikin kasar ta Nijar.
Hadin kai don kariyar kasa da mutuncinta babbar dubarar da ake bukata, domin hakan na nuni da cewa magabatan na da cikakkir fahimta da hangen nesa na abubuwan da ke faruwa na barazanar tsaro na zamani, wanda ta haka ne ma cikin wanan hadaka ta kungiyar hadin kan kasashen Sahel, ake ganin samar da wata rundina ta hadin gwiwa da ta kumshi sojoji kimanin dubu biyar, wani bangare ne na kasancewa cikin shirin ko ta kwana a fannin tabbatar da tsaro a yankin, wanda ake ganin ya kyautu yan kasa kowa daga nashi bangare ya horu da so da kuma kishi a kasarsa.
Ga masu lura da al'amura na yau da kullum, kuma ganin halin da ake ciki a sassa daban-daban na duniya musamman a wannan yanki na yammacin Afrika, inda matsalar tsaro ke kamari, daukan irin wannan doka ka iya wajabta idan aka dauki mataki na fadakar da yan kasa ta hanyar shirya taruka na gamgami.
Wannan yunkurin zai karfafa wa al'umma a fadin kasa kishin kasa da yadda kowa zai san irin nauyin da ya rataya don gama kai da yin taka tsantsan cikin salo. Kuma an dauki wannan mataki ne daidai tsarin dokoki na kundin tsarin mulki na sabuwar tafiyar da Nijar din ta sa wa gaba. Da kuma doka mai lamba 30 ta ran 31 ga watan Disamba a 2002 da ta yi magana kan tsara harkokin tsaron kasa, lamarin da ke nuni da cewa matakin na bisa kan tsari na doka ba wai abu ne da aka kirkiro kai tsaye ba illa kawai a yi taka tsantsan daga bangaran gwamnati na ganin wasu ma'aikatan basu bata rawar da tsalle ba.
Wannan dabara karfafa tsaron kasa tare da yan kasa, ta dogara ne kan tsarin kariya da rigakafi, a daidai lokacin da ake ganin cin zarafi da keta haddi na kasashe daga wasu manyan kasashe a kasancewa wani babban kalubale ga dokokin kasa da kasa. Hakan ya sanya magabata irin su shugaba Tiani na Nijar da takwarorinsa na AES da a kullum yaumin ke yin hannunka mai sanda ga al‘umominsu, ke cikin shirin ko ta kwana a matsayin rigakafi ya fi magani.