Larabawa na sawun gaba a gasar zakarun Afirka
February 16, 2026
Wasannin mako na shida na gasar zakarun Afirka ta kwallon kafa sun gudana a karshen mako, lamarin da ya kawo karshen matakin rukuni tare da tantance kungiyoyi takwas da suka kai zagayen kwata fainal.
Daga cikin wadanda dama ake kyautata wa zato, har da RS Berkane ta Maroko, da Espérance Tunis, da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu, yayin da a daya hannun kuma, kunnen doki ba tare da ci kwallo ba tsakanin Al Ahly ta Masar ya bai wa AS FAR ta Maroko damar samun gurbin shiga zagayen kusa da kusa da na karshe. Ita ma Al Hilal ta Sudan ta ba da mamaki wajen hayewa mataki na gaba,
Dama dai a nata bangare, Pyramids FC ta Masar ta riga ta tabbatar da matsayinta a zagayen kwata fainal da maki 13 sakamakon nasara da ta samu a sauran wasanni kafin na karshe. Hasali ma, ta doke Power Dynamos FC da ci 3-1 a cikin kwanciyar hankali, yayin da Stade Malien ta sha kashi a hannun Simba SC 0-1 ta tanzaniya, amma bai hana ta cancantar shiga mataki na gaba ba. Maimakon haka ma, Esperance Tunis ta yi amfani da damar bayan da ta doke Petro Luanda 2-0 wajen samun tikiti.
A takaice dai, kungiyoyi biyar na yankin Maghrib ne suka kai matakin kwata fainal na champions Leaugue na Afirka da kuma uku daga Kudu da Sahara.
Kuma gobe Talata ne hukumar kwallon ƙafa ta Afirka (CAF) za ta gudanar da bikin fitar da jadawalin zagayen kwata fainal na gasar zakarun Afirka da kuma gasar cin kofin Confederation.
A gasar Confederation Cup ta kwallon kafar Afirka kuwa, kungiyoyin da suka cancanci shiga zagayen kwata fainal sun hada da USM Alger ta Aljeriya, da Wydad Casablanca ta Maroko, da Chabab Riadhi Belouizdad, da Zamalek ta Masar. Sauran kungiyoyin sun hada da OC Safi, AS Maniema, da Otoho d'Oyo ta kwango, Al Masry ta Masar. Za a fara zagayen farko na kwata fainal ne a ranar 15 ga Maris, yayin da za a buga zagaye na biyu a ranar 22 ga Maris 2026.
Habaka wasan tamaula tsakanin 'yan mata a Nijar
Yanzu kuma za mu nufi Jamhuriyar Nijar, inda hukumar kwallon kafa ta FENIFOOT ke kokari wajen habaka wasan tamaula a tsakanin mata da 'yan mata kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da takwarta ta Afirka CAF suka bukata. Saboda haka ne ta shirya gasar kwallon kafa ta mata tsakanin na babban birnin Niamey da na Agadez. Duk da cewa 'yan matan Agadez ba su yi nasara ba, amma sun dauki wasan a matsayin dabarar karfafa wa mata gwiwa domin sun rungumi kwallon kafa duk da irin kalubale da yake cin wasan.
Kungiyoyi shida sun yi nasara a gasar Bundesliga
A nan gida Jamus kuwa, kwallaye 33 ne aka zura a wasannin mako na 22 na gasar kwallon kafa ta Bundesliga, inda kungiyoyin shida suka samu nasara a wasanni da suka buga a gida, ciki har da Bayer Leverkusen da ta yi wa FC St. Pauli dukan kawo wuka ci 4-0. Wannan ya ba wa Leverkusen damar hawa matsayi na 6 a teburi da maki 39.
Amma dai har yanzu Yaya-babba Bayern Munich tana kan gaba da maki 57 bayan da ta samu nasara da ci 3-0 a kan Werder Bremen. Harry Kane ya zura kwallaye biyu a rabin farko, wanda ya kawo jimillar kwallayensa zuwa 26 a wasanni 22 a bana, yayin da dan wasan tsakiya Leon Goretzka ya zura kwallo na uku bayan da aka dawo hutun rabin lokaci. Sai dai, Werder Bremen na ci gaba da kasancewa a rukunin 'yan baya ga dangi a matsayi na 16 da maki 19.
A nata bangaren, Borussia Dortmund ta farfado a wasanta da Mainz inda ta zura kwallaye hudu da kai, ciki har da guda biya da Serhou Guirassy na Guinea ya zura. Ita dai Yaya-karama Dortmund ta ci gaba da kasancewa ta biyu a teburin Bundesliga da maki 51, yayin da TSG Hoffenheim da ta doke Freiburg da ci 3-0 take a matsayi na uku da maki 45. Ita kuwa Stuttgart tana biya mata baya a matsayi na hudu da maki 42.
Amma RB Leipzig da ke a matsayi na biyar a teburin Bundesliga ta yi tuntube inda ta yi kunnen doki da Wolfsburg 2-2 sakamakon farke kwallo na biyu a minti na 88, lamarin da ya bakanta ziciyar kocin Wolfsburg Daniel Bauer:
"Leipzig ta mamaye rabin farko na wasan. Ya wajabta a gare mu mu kare kanmu, mun yi wannan kokarin yi duk da cewa mun sha wahala. A lokacin da ke jagorantar wasa da 2-1 a minti na 88, mun fara tunanin nasara, amma Leipzig ta yi amfani da damarta ta karshe. Amma barin wannan filin wasa na Leipzig da karin maki yana da mahimmanci."
Sai dai VfL Wolfsburg ta ci gaba da kasancewa a matsayi na 15 da maki 20, yayin da FC St. Pauli da FC Heidenheim ke matsayi na 17 da na 18.
Ana ci gaba da samun lambobi a gasar Olympics na kankara
Gasar Olympics ta hunturu ta duniya na ci gaba da gudana a Milano Cortina na kasar Italiya, inda baya ga tsere kan kankara da hockey na kankara da tsalle kan kankara, da kuma wasan motsa jiki na soja, za a gudanar da zamiyar kankara a rana ta 13 da fara gasar.
A halin yanzu dai, kasar Nowa ce ke kan gaba da yawan lambobi 26 ciki har da zinare 12 da azurfa 7 da tagulla 7. Sai kuma Italiya mai biya mata baya da lambobi 22 ciki har da zinare 8 da azurfa 4 da tagulla 10, yayin da Amurka ke biya mata baya da lambobi 17 ciki har da zinare 5.
Ita kuwa Netherland tana a matsayi na hudu da lambobi 11, yayin da Sweden ke biya mata baya. A nata bangaren, Faransa na a matsayi na shida da lambobi 15 ciki har da zinare 4, yayin da Jamus ke a matsayi na bakwai da lambobi 15 ciki har da zinare 4 da azurfa 6 da tagulla 15.
Kasar da ta kasance 'yan baya ga dangi a halin yanzu ita ce Beljiyam mai lamba daya tilo ta tagulla inda ta kasance a matsayi na 25.
Tennis: Francisco Cerundo ya lashe gasar ATP 250
A fagen tennis, bayan shan kaye sau biyu a wasan karshe, dan wasan Argentina Francisco Cerundo ya lashe gasar ATP 250 a Buenos Aires a karon farko a rayuwarsa, inda ya doke Luciano Darderi na Italiya da ci 6-4, 6-2 a ranar Lahadi. Idan za a iya tunawa dai, yayi rashin nasara a wasan karshe a 2021 a hannun Diego Schwartzman da kuma Joao Fonseca dan kasar Brazil a bara.
Amma a bana, Francisco Cerundo mai shekaru 27 ya lashe gasarsa ta hudu amma a wannan karon a garinsu, lamarin da ya danganta da cikan buri saboda ya "son yin nasara a gida a gaban abokai da iyalinsa."
A nasa bangaren Luciano Darderi, da ya cika shekaru 24 a ranar Asabar, ya yi wasan karshe na biyar ke nan inda ya lashe hudu na farko. Amma duk da rashin nasara dan kasar Italiyan ya kasance a matsayi na 21 a duniya a ranar Litinin a sabon jadawalin ATP, wanda shi ne mafi kyawun matsayi a tarihin aikinsa.
A rukuni mata na tennis kuwa, Victoria Mboko 'yar kasar Kanada mai shekaru 19 ta shiga cikin jerin 'yan wasa 10 mafiya shahara a duniya, kwana daya bayan ta kai wasan karshe na WTA 1000 da aka yi a Doha, wadda Karolina Muchova ta lashe, kuma ta hau matsayi na 11 na jadawalin ATP.
Amma dai har yanzu Aryna Sabalenka tana ci gaba da jan zarenta a matsayi na daya, yayin da Iga Swiatek ke biya mata baya a matsayi na biyu, ita kuwa Elena Rybakina take a matsayi na 3 bayan da Mboko ta doke a wasan kwata fainal a Qatar.
Ita kuwa Amanda Anisimova, da aka karbe kofin gasar Doha a hannunta ta samu komabaya inda ta baras da matsayi biyu i zuwa na shida, lamarin da ya ba Coco Gauff da Jessica Pegula damar hawa matsayi na 4 da na 5.