1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana za ta kwaso daruruwan 'ya'yanta daga Afirka ta Kudu

May 13, 2026

Ghana ta shirya kwaso wasu ‘yan kasarta daga Afirka ta Kudu bayan tashe-tashen hankula da suka shafi kyamar baki a wasu yankuna. Gwamnati ta ce tana daukar matakan gaggawa don kare lafiyar ‘ya'yanta a gida da waje.

https://p.dw.com/p/5DjPS
Yadda ake kama mutane yayin zanga-zangar adawa da baki a Afirka ta Kudu.
Yadda ake kama mutane yayin zanga-zangar adawa da baki a Afirka ta Kudu.Hoto: Zhai Jianlan/Xinhua/IMAGO

Ghana ta sanar da shirin kwaso ‘yan kasarta su 300 daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren kyama da ake kai wa baki daga wasu kasashen Afirka.

Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta ce mutane da dama sun nemi taimakon gwamnati domin komawa gida, yayin da gwamnatin kasar ta sha alwashin kare lafiyar ‘yan kasarta a gida da waje.

Hare-haren na kyamar baki a Afirka ta Kudu, sun fusata shugabanni da hukumomi a kasashen nahiyar Afirka da dama.

Duk da cewa hukumomin Afirka ta Kudu sun yi Allah wadai da hare-haren, sun nuna matsalar shige-da-fice ba bisa ka'ida ba da zama cikin dalilan da ke haddasa tashin hankalin.

Kasashe irin su Kenya da Malawi da Lesotho gami da Zimbabwe, sun gargadi ‘yan kasarsu da su yi taka-tsantsan, yayin da Najeriya ta ce akalla ‘yan kasarta 130 su ne suka yi rajistar komawa gida daga Afirka ta Kudun.