Darasin rayuwa: Hadarin ababen hawa fitina ga rayuwa
August 11, 2023
Talla
Wannan lamarin na hadasa mummunan illa ga rayukan wadanda Allah ya tarfa wa garinsu nono da kasancewa suna da raguwar numfashi a duniya. Duk da yake babu wasu cikakkun alkaluman da suka bayyana a zahiri wadanda suka jikkata sakamakon hadduran a Najeriya kawai matsalar ta kashe mutane fiye da dubu tara da rabi a bara baya ga wasu dubban da suka jikkata.
Hadurran ababnen zirga-zirga na zama sanadin rasa wani bangare na sassan jiki
A jamhuriyar Nijar rayukan mutuane fiye da 1200 ne suka salwanta ta hanyar hadurran na ababen hawa a shekara ta 2021, wannan ya sa kasar ta kasance ta bakwai a wannan lokaci daga cikin jerin kasashen Ecowas masu fama da hadurran ababen hawa a yammacin nahiyar Afirka.