Hamas ta fara sako Isra'ilawa da ke hannunta
October 13, 2025
An fara sakin sauran fursunoni 48 da Hamas ke rike da su a Gaza, inda kafafen yada labaran Isra'ila suka ruwaito cewa an mika mutane bakwai daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross da safiyar Litinin.
ICRC ta fada a cikin wata sanarwa cewa ta fara aiwatar da matakai da dama don saukaka sakin mutanen da kuma jigilar fursunoni da wadanda ake tsare da su a matsayin wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
Amurka ta gabatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Gaba daya, ana sa ran Isra'ilawa 20 da ke raye za a sako a ranar Litinin, ciki har da Alon Ohel, da tagwaye Ziv da Gali Berman 'yan Isra'ila da kuma Jamus.
An kai wannan matakin ne bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas sakamakon shiga tsakanin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi.
A daya bangaren kuma za a sako Falasdinawa kusan dubu biyu da ke gidajen yarin Isra'ila daban-daban a ranar Litinin kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
Iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza sun hallara a sansanin sojojin Isra’ila da ke Re’im tun da sassafe a ranar Litinin, inda ake sa ran za a kai fursunonin bayan sakosu.
Kungiyar Hamas ta fara mika fursunonin ga ma’aikatan ICRC daga tsakiyar Gaza, sannan za a ci gaba daga yankin Khan Younis da kuma wasu sassan yankunan Gaza daban-daban. kafin a kaisu cikin Isra’ila.
Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza
Isra’ila ta ce adadin mutanenta da za a sako zai kai 20 a yayin da suma Falasdinawa kusan 2.000 za su shaki iskar 'yanci.
A sansanin Re’im, za a hada wadanda aka sako da danginsu da duba lafiyarsu sannan a ba su damar yin wanka da sauya kaya kafin a tashi da su zuwa asibitoci domin ci gaba da kula da lafiyarsu.