Hamas ta mika wa Isra'ila sunayen fursunoni domin musaya
October 8, 2025
Kungiyar Hamas ta ce ta musanya jerin sunayen fursunonin da ake son a sako da gwamnatin Isra'ila a wani bangare na tattaunawar da ake ci gaba da yi na ganin an kawo karshen rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.
Sanarwar Hamas ta nuna cewa jerin sunayen sun hada da Isra‘ilawan da mayakan Hamas ke rike da su a Gaza, da kuma Falasɗinawa da ke cikin gidajen yari a Isra'ila.
A karkashin shirin zaman lafiya da Shugaban Amurka Donald ya gabatar, Isra'ila za ta saki kusan Falasɗinawa 250 da ke da hukuncin dauri na rai-da-rai, tare da kimanin wasu 1,700 da aka kama bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, 2023.
Tattaunawar a kaikaice tsakanin Isra'ila da Hamas kan wannan shirin na Trump na ci gaba a birnin Sharm el-Sheikh da ke gabar tekun Bahar Maliya a Masar, tun daga ranar Litinin.