1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan rashin bayyanar sabon jagoran Iran

Mahmud Yaya Azare AH
March 12, 2026

Mako guda bayan zaɓen Mojtaba Khamnaei a matsayin sabon jagoran addinin Iran, ana ci gaba da cece-kuce kan rashin bayyanarsa a bainar jama'a.

https://p.dw.com/p/5AHKv
Tutar Iran
Tutar IranHoto: Aleksey Butenkov/Zoonar/dpa/picture alliance

Wasu majiyoyi na cewa an boye shi ne domin  kariya daga yiwuwar hare-hare ko yunƙurin kashe shi, musamman a wannan lokaci da kasar ke cikin halin yaki,Isra'ila da Amurka kuma ke barazanar kashe,kamar yadda Muhsen Rafeiz ,daya daga cikin jami,an liken asirin kasar ke fadi.

Masana harkokin siyasa suna ganin cewa rashin bayyanar sabonjagoranna iya yin tasiri ga yanayin yaƙin da kasar ke yi. A irin wannan lokaci, bayyana jagora a bainar jama'a kan zama wata hanya ta karfafa gwiwar jama'a da kuma dakarun soja.

Amma a gefe guda, wasu na ganin cewa Iran na iya bin wata dabara ta tsaro, wato kare sabon jagoran domin tabbatar da cewa tsarin shugabanci bai shiga wani sabon rudani ba kamar yadda Khatamy Husainy ,masani kan harkokin tsaro ya bayyana:

''Idan aka duba tarihin siyasar Iran, jagoranci na da muhimmiyar rawa wajen hada kan al'umma a lokacin rikici. Rashin bayyanar jagora na iya haifar da tambayoyi, amma kuma wani lokaci hakan na iya zama matakin tsaro idan ana ganin akwai barazana.”

Tun kafin ya zama jagora, Mujtaba Khamnaei ba kasafai yake bayyana a bainar jama'a ba. A tsawon shekaru yana aiki ne a bayan fage a cikin tsarin siyasar Iran, musamman a kusa da ofishin mahaifinsa.

Saboda haka wasu masu sharhi suna ganin cewa wannan salonna iya ci gaba, inda zai fi yin aiki a cikin tsarin gwamnati ba tare da yawan fitowa fili ba.

A halin yanzu dai, al’ummar Iran da ma duniya na jiran lokacin da sabon jagoran zai bayyana a bainar jama'a domin gabatar da jawabi ko kuma bayyana manufofinsa kan rikicin da kasar ke ciki.

Masana sun ammanar cewa, duk wani mataki da zai dauka a  kwanaki masu zuwa na iya yin tasiri mai girma ga makomar yaƙin Iran da Amurka da Isra’ila.

 

 

Wannan labarin an wallafa tare da hoto daga kamfanin dillancin labaran SalamPix. An cire hoton ranar 12 ga watan Maris 2026, bayan an sanar da cewa hotonan SalamPix akwai damuwa kan yuwuwar an jirkita.