Hare-hare a Mali sun hargitsa kasar
April 27, 2026
Kasar Mali tana jimamin rashin ministan tsaronta Sadio Camara, wanda harin da aka kai gidansa a ranar Asabar ya salwantar da ransa da na iyalansa. Kungiyar JNIM da ke tsaurin ra'ayin Islama ce ta dauki alhakkin kai jerin hare-hare a sassan kasar Mali, bisa hadin gwiwar kungiyar fafutuzkar 'yantar da Azawad. Wadannan hare-hare da ba a taɓa ganin irinsu ba sun jefa kasar cikin firgici.
Hare-haren da aka tsara
Muhimman birane biyar na kasar Mali ne suka fuskanci hari a lokaci guda ciki har da Sévaré da Gao da Bamako da Kati da ke zama cibiyar gwamnatin rikon kwarya ta Assimi Goita. Sai kuwa birnin Kidal da ya kasance tungar gwada kwajin karfin sojojin Mali, saboda dakarun gwamnati sun kwace birnin ne daga hannun 'yan Abzunawa a shekarar 2023.
Ministan tsaron Mali Sadio Camara ya zama daya daga cikin wadanda suka rasu rayukansu a ranar Asabar, 25 ga Afrilu, a lokacin harin ta'addanci da aka kai gidansa da ke Kati. Ministan cikin gida da ke magana da yawun gwamnatin Mali Brigadier Janar Ousmane Coulibaly ne ya tabbatar da mutuwar babban jami'in a kafar talabijin ta kasa, tare da ware kwanaki na zaman makoki.
Zaman makoki da tsaurara matakan tsaro
Bamako ta ayyana zaman makoki na kwana biyu a fadin kasa, wanda ya fara a wannan Litinin, don girmama wannan babban jami'in da ya ba da gudunmawa wajen kafuwar gwamnatin Assimi Goita. Bugu da kari, dokar hana fita ta dare ta awanni 72 ta fara aiki tun daga daren Asabar a gundumar Bamako, daga karfe 9:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe. Sannan wannan dokar hana fita ta shafi mazauna Koulikoro a yammacin kasar, yanki na biyu mafi girma a kasar.
Sakamakon tsaurara matakan tsaro da aka yi, shingayen bincike sun mamaye manyan hanyoyin Bamakao, musamman ma a gaban ciboyiyn 'yan sanda, da hedikwatar sojoji, da kuma tashar watsa labarai da talabijin ta kasa ta Mali ORTM.
Sai dai a Kati, da ke zama cibiyar mulkin sojoji, a tazarar kimanin kilo-mita 15 (goma sha biyar) daga Bamako, shaidu sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe a ranar Lahadi.
Kura ta lafa
Bayan hare-haren da masu ikirarin jihadi na JNIM da ke da alaka da Al-Qaeda suka kai a ranar Asabar, daga bisani rundunar sojojin Mali (FAMa) ta yi arangama da su na tsawon awanni da yawa. Amma kura ta lafa tun daga ranar Lahadi a birnin Mopti da kuma Sévaré da ya kunshi sansanonin sojoji mafi muhimmanci a kasar.
An kuma bayar da rahoton fada a Kidal tsakanin sojojin Mali da 'yan awaren FLA, wadanda Bamako ke dauka a matsayin 'yan ta'adda. Su ne ma ke ikirarin sake kwace birnin.