Labarin Wasanni: PSG ta lashe kofin zakarun Turai
June 1, 2026
'Yan wasan Paris Saint-Germain PSG ta Faransa sun samu gagarumar tarba a ranar Lahadi, bayan sun zama zakarun Turai a karo na biyu a jere. PSG ta doke Arsenal da ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a fafatawar da suka yi a birnin Budapest. Mai horaswa Luis Enrique da 'yan wasansa sun yi rangadi a titunan birnin Paris zuwa dandalin Champ de Mars kafin su isa filin wasa na Parc des Princes, inda dubban magoya baya suka hallarci bikin murnar mai taken "Back2Back".
Sai dai murnar ta samu tangarda sakamakon tashe-tashen hankula da suka barke a wasu wurare na birnin Paris, lamarin da ya kai ga kama mutane 890 a cewar ministan harkokin cikin gida na Faransa. Wannan adadin, ya zarta na shekarar da ta gabata a lokacin da kungiyar ta lashe kofin a karon farko da kusan kashi 45 cikin 100. Haka kuma jami'an tsaro 178 sun samu raunuka, sakamakon hare-hare da jifansu da abubuwa da aka yi yayin bukukuwan murnar. Sai dai shugabannin kungiyar ba su takaita kan murna kawai ba, domin tuni sun fara shirye-shiryen shiga kasuwar sayen 'yan wasa ta lokacin bazara da nufin kara karfafa tawagar tare da burin ci gaba da kare kambun da suka samu.
Idan muka nufi Ingila duk da rashin nasara da Arsenal ta yi a wasan karshe na gasar zakarun Turai a gaban PSG dubban magoya bayan kungiyar sun fito kan titunan arewacin birnin London, domin murnar lashe gasar Premier League da Arsenal din ta dauka a karon farko cikin shekaru 18. An kiyasta cewa mutane kusan miliyan daya ne suka halarci faretin da aka yi a ranar Lahadi, wanda ke zama daya daga cikin manyan tarukan murnar kwallon kafa da aka gani a kasar Ingila cikin 'yan shekarun nan. Magoya bayan Arsenal sun yi ta rera wakoki suna ambaton sunan kungiyar, a cikin yanayi na farin ciki da annashuwa.
A shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2026 da za a fara daga ranar 11 ga watan Yuni a Amurka da Kanada da Mexico, wasu daga cikin kasashen da suka samu tikitin halartar gasar sun fafata wasannin sada zumunta a karshen makon jiya. Tawagar Mannschaft ta Jamus ta lallasa Finland da ci 4-0 a fafatawar da suka yi a birnin Mainz, inda dan wasa Deniz Undav ya jefa kwallaye biyu yayin da takwarorinsa Florian Wirtz da Jamal Musiala suka ci kwlallo guda-guda.
Ita ma tawagar 'yan kwallon Amurka mai masaukin baki ta doke zakarun Afirka na Senegal da ci 3–2, a barje gumin da suka yi. Brazil ma ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen yi wa Panama luguden kwallaye ci 6-2, a karawar da tauraron dan wasa Neymar bai buga ba saboda fama da rauni. A wani labarin kuma tawagar Bafana-Bafana ta Afirka ta Kudu ta jinkirta tafiyarta zuwa kofin duniya, saboda matsalolin samun takardar izinin shiga kasa wato Visa ga wasu 'yan wasa da kuma jami'anta. Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta kasar ta ce, an warware mafi yawan matsalolin kuma ana sa ran tawagar za ta tashi zuwa sansanin karbar horo na Mexico.
Yayin da ake shirin bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara wato Mercato, manyan kungiyoyin Turai sun fara neman sababbin taurari domin karfafa kungiyoyinsu. Bayan lashe kofin zakarun Turai, rohotanni na cewa PSG ta Faransa na kyalla ido ga dan wasan gaba na Argentina Julián Álvarez da kuma matashin dan Faransa Éli Junior Kroupi. Ita kuwa Real Madrid da ta yi farar shekara a bana, na ci gaba da bibiyar dan wasan baya na Faransa Ibrahima Konaté wanda ake rade-radin cewa babu tabbas game da sabunta kwantaraginsa da kungiyar Liverpool. Sai dai 'yan farin gidan na hamayya da Bayern Munich ta Jamus, wadda ita ke sha'awar cefano Konaté. Ita ma dai Barcelona zakarar LaLiga ta Spain ta dage kan neman 'yan wasa sababbin, sai dai ta fi mayar da hankali a kan dan wasan Atletico da Madrid Julián Álvarez.
A gasar kwallon Tennis ta Roland-Garros da ke gudana a yanzu haka a Faransa matashin dan wasan Brazil João Fonseca mai shekara 19 na ci gaba da ba duniya mamaki, bayan ya doke tsohon wanda ya kai wasan karshe sau biyu Casper Ruud tare da samun tikitin zuwa zagayen quarter fainal na Grand Slam karo na farko a rayuwarsa. A mataki na gaba zai kara da dan wasan Jamhuriyar Czech Jakub Menšík. A bangaren mata kuwa an samu babban abin mamaki, inda 'yar Ukraine Marta Kostyuk ta fitar da tsohuwar zakarar gasar har sau hudu Iga Świątek ta Poland. Wannan lamari na tabbatar da cewa za a samu sabuwar zakarar Roland-Garros a bana.
A fagen gasar tseren motoci ta Formula 1 kuwa, za a gudanar da zagayen Grand Prix de Monaco na 2026 a titunan Monte Carlo na Faransa a ranar bakwai ga watan Yuni. Sai dai sababbin dokoki na fasaha da aka shigo da su za su karawa gasar ta bana zafi, inda ake hasashen fitattun 'yan tsere na iya gamuwa da gagarumar hamayya.
Labari: Mohamed Tidjani Hassane
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar