Hari ya halaka mutane 17 a Sudan
March 11, 2026
A kasar Sudan wani jirgin maras matuki da ake zargin mayakan kungiyar RSF da harbawa kan wata makaranta da cibiyar kula da lafiya ya halaka mutane 17 a yankin kudancin kasar, gabili yara mata 'yan makaranta. Kimanin mutane 10 suka jikata sakamakon harin. Babban jami'in kula da kiwon lafiya na lardin White Nile ya tabbatar da labarin.
Yaki ya barke a shekara ta 2023
Tun watan Afrilun shekara ta 2023 kasar Sudan ta fada cikin yakin basasa tsakanin sojojin gwamnati da mayakan rundunar RSF. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa yakin ya lakume rayukan fiye da mutane 40,000, inda kungiyoyin masu zaman kansu ke cewa alkaluman sun wuce haka.
Akwai kuma zargin aikata miyagin laifukan yaki a rikicin na kasar ta Sudan wajen cin zarafin mata da sauran fararen hula, da kashe-kashe marasa tushe.