1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hari ya halaka mutane 73 a Sudan ta Kudu

Suleiman Babayo LMJ
March 30, 2026

'Yan bindiga sun hallaka mutane 73 a wajen hakar ma'adanai da ke kasar Sudan ta Kudu, yyin da wasu mutane 25 suka jikata, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

https://p.dw.com/p/5BOyI
Sudan ta Kudu
Sudan ta KuduHoto: Luis Tato/AFP

An tabbatar da mutuwar mutane 73 sakamakon harin 'yan bindiga a wajen da ake hakar ma'adanai na kasar Sudan ta Kudu, da ke wajen birnin Juba fadar gwamnatin kasar. Akwai wasu mutanen 25 da suka samu raunika sakamakon wannan hari.

Hukumomi sun tabbatar da harin

Mataimakin shugaban kasar James Wani Igga ya tabbatar da faruwan lamarin cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Litinin.

Jinkai a Sudan ta Kudu
Jinkai a Sudan ta KuduHoto: Samir Bol/Anadolu Agency/IMAGO

Yankin da lamarin ya faru an dade ana hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, da kuma samun tashe-tashen hankula, inda majiyoyin diflomasiyya ke cewa mutanen da suka mutu sakamakon farmakin na 'yan bindagan sun kai 86.

Ita dai Sudan ta Kudu da ta samu 'yanci daga kasar Sudan a shekera ta 2011, ta sahun gaba na kasashen 'yan rabbana ka wakatamu, ga kuma tashe-tashen hankula da suka yi katutu a kasar.