SiyasaGabas ta Tsakiya
Harin Isra'ila a Sana'a babban birnin Yemen ya halaka mutane
August 25, 2025Talla
Harin Isra'ila a Sana'a babban birnin Yemen ya halaka mutane 6 a jiya Lahadi, tare da jikkata wasu 86, kamar yadda 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran suka tabbatar.
Harin na Isra'ila na zama ramuwar gayya ga hare-haren makamai masu linzami da Houthi ke kai wa jiragen ruwan Isra'ila masu ratsawa ta kogin Baharmaliya, wanda Houthin ke ikirarin cewa tana ramawa Falasdinawan Gaza ne.
Karin bayani:Jamus ta bukaci a dakatar da yunwa a Gaza
Wasu hotuna da ma'aikatar tsaron Isra'ila ta wallafa da ranar jiya Lahadi, sun nuna yadda Firaminista Benjamin Netanyahu da ministan tsaro Israel Katz da kuma babban hafsan sojin kasar Eyal Zamir ke nazartar yadda harin na Yemen ke gudana.