Iran ta sha alwashin toshe mashigin Hormuz gaba daya
March 22, 2026
Tehran ta ce muddin aka kai wa tashoshin makamashinsu hari to za su dauki matakin rufe mashigin.
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa, mashigin ruwan na Hormuz dake da matukar muhimmanci ga jigilar man fetur a duniya, za a toshe shi kuma za a bude shi ne kawai bayan sun kammala aiki sake gina wuraren da aka lalata.
Tuni dai jigilar makamashi a mashigin ruwan ke fuskantar cikas tun bayan barkewar yakin kawance na Amurka da Isra'ila a kan Iran, wanda ya sa farashin man fetur a kasuwannin duniya ya yi tashin gouron zabi.
A ranar Asabar ce shugaban Amurka Donald Trumpya yi barazanar lalata tashoshin wutar lantarki na Iran idan ba a bude mashigin Hormuz a cikin sa'o'i 48 ba a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta na Truth Socials, barazanar da Iran ta sha alwashin mayar da martani a kan kasashen Larabawa dake da sansanonin Amurka.