Iran tana nazarin tayin Amurka na tsayar da yakin da suke yi
May 21, 2026
Iran ta sanar da cewa tana nazartar tayin da Amurka ta yi ma ta na baya bayan nan, kan shirin kawo karshen yakin da kasashen biyu ke gwabzawa, bayan da aka jiyo shugaba Donald Trump na bai wa Tehran kwanaki kalilan, gabanin samun amsa, ko kuma ya koma fagen daga, idan har ta ki aminta da sharuddan da ya gindaya mata.
Karin bayani: Iran tana shirye da duk wani hariin Amurka
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ce ta tabbatar da hakan, ta bakin kakakinta Esmaeil Baghaei, kamar yadda kafar yada labaran kasar mai suna Nour News ta rawaito.
Kasar Pakistan, wadda ke taka rawar daidaita tsakani, na ci gaba da kai komo, wajen ganin Tehran da Washington sun cimma sulhu a tsakaninsu, inda ministan harkokin cikin gida na kasar Mohsin Naqvi ya ziyarci birnin Tehran ranar Laraba, domin ci gaba da fafutukar kulla yerjejeniyar sulhu tsakanin Amurka da Iran.
Karin bayani: Trump ya sake yin barazanar shafe Iran idan ta ki sulhu
Tun a farkon wannan mako dakarun juyin-juya-halin Iran suka yi gargadin cewa, matukar aka sake kai wa kasar farmaki, to tabbas za su fadada yakin har ya wuce yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin ramuwar gayya.
Karin bayani: G7 na kukan yadda yakin Iran ya rusa tattalin arzikin duniya
A gefe guda Iran ta aiwatar da hukuncin kisa ga mutane biyu da take zargi da ayyukan ta'addanci da tona asirinta.
Mutanen da aka kashe, wadanda suka hada da Ramin Zaleh da kuma Karim Maroufpour, wadanda ta ce sun kafa wata kungiyar ta'addanci, domin gurgunta tsarin tsaron kasar.
Wannan na cikin rahoton da kafar yada labaran Iran ta Tasmin ta rawaito a wannan Alhamis.