1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta yi barazanar komawa filin daga

October 16, 2025

Isra'ila ta ce za ta koma yaki idan har Hamas ba ta mutunta shirin zaman lafiya da Trump ya gabatar kan yakin Gaza ba.

https://p.dw.com/p/524wt
Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz
Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz Hoto: Menahem Kahana/AFP/Getty Images

Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da hukumomin kasar suka karbi gawarwakin wasu fursunonin yaki guda biyu daga kungiyar Hamas, inda ya ce har yanzu suna bukatar kungiyar ta Hamas da ta mutunta yarjejeniyar da aka cimma wajen mika musu sauran gawarwakin ragowar mutanen da ke hannunta.

Karin bayani:Mutanen Isra'ila 20 da Hamas ta saki sun isa birnin Tel-Aviv

Tun bayan fara aiwatar da sabuwar taswirar zaman lafiya ta Shugaba Trump, kungiyar Hamas ta mika fursunonin yaki 20 ga Isra'ila, yayinda hukumomin Tel Aviv suka mika kimanin dubu 2,000 ga Falasdinawa. Kafin mika gawarwakin mutanen biyu, Hamas ta riga ta mika 28 ga gwamnatin Isra'ila.