1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jakadan Sudan ya caccaki rawar da EU ke takawa a yakin Sudan

October 30, 2025

Jakadan Sudan a kungiyar Tarayar Turai Aldelbagi Kabeir ya kalubalanci EU kan rashin taka rawar gani a yakin Sudan, wanda hakan ya saba da abin da suka yi tunani.

https://p.dw.com/p/52r4Z
Wasu daga cikin matan da suka kauracewa El-Fasher da dakarun RSF suka kai farmaki
Wasu daga cikin matan da suka kauracewa El-Fasher da dakarun RSF suka kai farmakiHoto: AFP/Getty Images

Jakandan ya furta hakan a wani taro da aka gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium, inda ya bukaci tallafin kungiyar EU da sauran kasashen duniya wajen ganin cewa sun dauki mataki kan rundunar kar-ta-kwana ta RSF da kuma wadanda ke goyon bayan su daga kasashen ketare.

Karin bayani:Shin ana iya kawo karshen rikicin Sudan?

Ambassada Aldelbagi Kabeir na daga cikin jami'an gwamnatin da ke bangaren Janar Abdel-Fattah Burhan da Firaminista Kamil al-Taib Idris, wadanda kasashen duniya ta amince dasu a matsayin halastattun shugabannin Sudan.

Karin bayani:EU ta fusata kan ta'asar RSF a el-Fasher

A baya bayan nan dai mutuna sama da 30,000 suka kauracewa yankin el-Fasher, sakamakon kwace iko da RSF ta yi da kuma luguden bama-bamai da hare-haren kan mai uwa da wabi da take kai wa a yankin.