1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Brazil na neman kara karfin dangantaka

April 19, 2026

Kasashen biyu na son kara karfafa alaka a bangarorin ci-gaban fasaha da tsaro da kasuwanci da kuma kare yanayi.

https://p.dw.com/p/5CRnx
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz da shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz da shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da SilvaHoto: Michael Kappeler/dts Nachrichtenagentur/IMAGO

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz na shirin karbar bakuncin shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva a birnin Hannover. Ana sa ran shugabanin biyu su bude taron baje kolin kasuwar masana'antu mafi girma a duniya a birnin. A ranar Litinin ake sa ran gwamnatocin kasashen biyu za su gudanar da taron tuntuba da nufin kara karfafa alaka, a bangarorin kasuwanci da tsaro da ci-gaban fasaha da bincike da kuma kare yanayi. 

Karin bayani: Jamus na neman kwararru daga Brazil

Za kuma su tattauna kan dokokin kasa da kasa, ciki har da matakin Amurka a kan Iran da Venezuela da kuma Cuba. Shugaba Lula da ke neman kujera ta dindindin a kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na fatan yin fito na fito da karfin ikon Shugaba Trump a siyasance.

A lokacin da yake tattaunawa da jaridar Der Spiegel, Lula ya ce ba a zabi Trump a matsayin basaraken duniya ba, don haka bai kamata ya ci gaba da yin barazana ga kasashe da yaki ba.