1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da China sun karfafa alakar dangataka

February 25, 2026

Kasashen Jamus da China sun jaddada bukatar karfafa dangantaka a tsakaninsu duk da bambancin ra'ayi da suke da su a wasu fannoni

https://p.dw.com/p/59OQl
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da shugaban China Xi Jinping
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da shugaban China Xi Jinping Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya shaida wa shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, a birnin Beijing a ranar 25 ga watan Fabrairun 2026 cewa ya kamata kasashensu su karfafa matakan sadarwa ta dabarun siyasa da kuma amincewa da juna.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke kara fuskantar rikice-rikice da sarkakiya.

Xi ya ce yana bai wa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu muhimmanci matuka.