Jamus: Sabbin manufofi kan yan gudun hijira
January 30, 2026
Yarjejeniyar Dublin ta tanadi cewar, mutanen da suka yi rijista a wasu kasashen Turai ko kuma sun riga sun nemi mafaka a can, za a iya tsare su a cibiyoyin masu neman mafaka na musamman har zuwa watanni uku. Da wadannan ka'idodi masu tsauri, gwamnatin tarayyar Jamus tana son saukaka mayar da 'yan gudun hijira gida da kuma tabbatar da cewar mutane ba za su iya buya ba, kafin lokacin korasu gida.
Duk da haka, shawarar ko za a kafa wadannan cibiyoyin a matsayin mafaka tana hannun jihohin kasar. Wajibi ne kuma a amince da sabbin ka'idoji a matakin majalisun zartarwa ta kasa, wadanda su ne ke wakiltar jihohin tarayya.
Karin Bayani: Jamus za ta karbi 'yan Afghanistan sama da 500
Sai dai a yayin aiwatar da wannan shiri ya kamata a guji matsalolin wahala gwargwadon iko. Masanin manufofin cikin gida na jam'iyyar SPD, Sebastian Fiedler ya ce, yana da matukar muhimmanci a kauce wa haifar da wahalhalun da za a iya kauce musu ga yara da iyalai, da kuma tabbatar da kare kungiyoyi masu rauni. Hakan a cewarsa yana nufin kada a tsare yara, da isasshen kula da lafiya, da kuma iyakance wajibcin iyalai su zauna a cibiyoyin mafaka. A matsyin doka, ya kamata a bar yara da iyalansu su bar wadannan cibiyoyi bayan watanni shida.
Mutanen da ke cikin tsarin mafaka da wadanda ke da izinin zama na dan lokaci, a basu damar yin aiki cikin sauri a nan gaba, sabanin yadda tsarin yake a baya na dole sai sun jira watanni shida, a mayar da shi bayan watanni uku kacal a nan gaba. Duk wanda ke zaune a Jamus ya kamata ya sami damar samun abin da zai iya kulawa da kansa, in ji kwararre kan manufofin cikin gida Fiedler.
Karin Bayani: Binciken yanayin rayuwar 'yan gudun hijira a Jamus
Bugu da kari, gwamnatin hadakar tana kuma son inganta kula da lafiya ga yaran 'yan gudun hijira, kuma a cikin watanni 36 na farkon kasancewarsu a kasar, a ba da damar gwaje-gwajen da basu takaita ga maganin ciwo da duba lafiyarsu ba. Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi Allah wadai da sabon tsarin mafaka. Mai magana da yawun manufofin shari'a na kungiyar goyon bayan masu neman mafaka, Wiebke Judith, ta yi kira ga 'yan majalisar dokoki da su cire batutuwan kare hakkin dan adam, kamar takunkumi kan 'yancin walwala da tsarewa daga dokar da yarjejeniyar da suka cimma kan aiwatar da tsarin na GEAS a Jamus, jam'iyyun da ke mulki suna daukan sabon salo mai tsauri kan masu neman mafaka.
A nan gaba, za a takaita wa 'yan gudun hijira barin cibiyoyin da aka ajiyesu tun daga farko, da farko da dare, sannan daga baya da har ma a rana. Bugu da kari, akwai barazanar tsara sabbin hanyoyin neman mafaka. Har ma yara da sauran mutane masu rauni ba a kebe su daga wannan ba. Sai dai a wannan fanni, dokar Jamus ta wuce gona da iri ga tanadi da kuma bukatun dokar EU, a cewar masu kare hakkin dan Adam.
Karin Bayani: Merz ya umurci a tsaurara tsaro a iyakokin Jamus
Gyaran da Tarayyar Turai ta amince da shi a lokacin bazara ta 2024 yana da nufin inganta tsarin mafaka na Turai, don kara rage kaura ba bisa ka'ida ba, da kuma hanzarta hanyoyin samun mafaka. A nan gaba, wadannan za su faru ne musamman a iyakokin kasashen EU. Babbar matsalar kawo yanzu ita ce, kasashe da ke da iyakoki da wasu kasashen waje, kamar Italiya, da Bulgaria, da Croatia, da Girka, ba sa karbar bakin haure da ke tafiya daga can zuwa wasu kasashen EU, duk da ka'idojin tarayyar Turai.