Jamus ta nemi Turai ta kare kanta bayan janye sojin Amurka
May 2, 2026
Jamus ta bukaci kasashen Turai su kara himma, domin dogaro da kai wajen karfafa tsaron nahiyar, sakamakon matakin da Amurka ta dauka na janye dakarunta dubu biyar daga Jamus, a matsayin martanin kin mara mata baya a yakinta da Iran.
karin bayani: Amurka ta janye sojinta daga Jamus bayan kin yakin Iran
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius, ya ce dama cin sun yi tsammanin ganin wannan mataki daga Amurka, kuma lokaci ya yi da Turai za ta tashi tsaye ta kare kanta da kanta, ta hanyar fadada rundunoninta na tsaro da samar da ingantattun makaman yaki.
Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ce ta fara tuntubar Amurka don jin yadda aikin janye sojojin nata zai kasance.
Karin bayani: Jamus ta shawarci Iran ta amince da sulhun yakinta da Amurka
Yayin da shi kuma firaministan Poland Donald Tusk ke nuna damuwa da wannan lamari, a daidai lokacin da kasarsa ke bukatar tabbacin kariyar tsaro daga Amurka da NATO, sanadiyyar yakin Rasha da ke gwabzawa da Ukraine.