Jamus ta shirya mika kadarorin Rasha wa Ukraine
December 18, 2025
Majiyoyin diflomasiyya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Jamus DPA cewa, shugaban gwamnatin Jamus na da niyyar amincewa bukatun Belgium da kuma mika kadarorin babban bankin Rasha da ke Jamus don tallafawa Ukraine.
Shugabannin kasashen Turai na taro a birnin Brussels da nufin lalubo mafita don biyan bukatun tattalin arziki da na soji na Ukraine na shekaru masu zuwa, a yayin da ta ke ci gaba da gwabza yaki da Rasha.
Hukumar Tarayyar Turai ta ba da shawarar samar wa Kiev tallafin kudi da yawansu ya kai Euro biliyan 210 na kadarorin Rasha da ke cikin Tarayyar Turai a matsayin rancen diyya, wanda daga ciki za a yi amfani da Euro biliyan 90 a bangaren bukatun kudi da tsaro a 2026 da 2027.
Gwamnatin Belgium ta dage kan cewa, dole ne dukkan kasashen EU da ke rike da kadarorin Rasha su shiga cikin shirin samar da kudaden tallafi wa Kiev, domin rage hadarin barin Belgium ta kasance wadda za a iya daukar matakan fansa a kanta ita kadai.