1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta soki Faransa da kin kashe kudin fannin tsaron Turai

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 16, 2026

Kasashen Turai da ke cikin NATO na fuskantar matsin lamba daga Amurka, domin kara hobbasa wajen samar da kudaden aiki.

https://p.dw.com/p/58qsR
Ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul
Ministan harkokin wajen Jamus Johann WadephulHoto: Ronka Oberhammer/DW

Jamus ta soki Faransa kan dungushen da take yi, wajen kashe kudi a fannin tsaro, inda ta yi kira ga Paris da ta kara azama a wannan bangare, don karfafa tsaron nahiyar Turai, lamarin da ke kara nuna rarrubwar kawunan da ke wakana a tsakanin kasashen biyu.

Ministan harkokin Jamus Johann Wadephul ya ce sau tari shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sha nanata bukatar kare 'yancin nahiyar Turai, to amma akwai bukatar a gani a kasa, kan abin da yake furtawa.

Kasashen Turai da ke cikin kawancen tsaro na NATO, na fuskantar matsin lamba daga Amurka, domin kara hobbasa wajen samar da kudaden da za a yi aiki da su domin habaka tsaron kasashen.

Karin bayani -Sweden za ta sayi tankokin yaki kirar Jamus

Shi ma shugaba Karol Nawrocki na Poland, ya nuna bukatar kasarsa ta samun makamin nukiliya na kashin kanta, la'akari da yadda Rasha ke zama gagarumar barazana ga kasarsa.

Ko da yake shugaban bai bayyana lokacin da ya kamata a ce burinsa na sa ya tabbata ba, to amma ya ce abu kalilan ka iya fusata Rasha a ko wane lokaci, hakan kuma kan kai ta ga mayar da martani mai zafi.

Karin bayani - Zelensky zai gana da shugabannin EU kan yakin Rasha

Poland na cikin kasashen kawancen tsaro na NATO da ke tallafawa Ukraine, domin kare kanta daga Rasha, wadda ta shafe shekaru hudu tana mamayarta.