SiyasaJamus
Jamus ta tsawaita dokar kullen corona
January 5, 2021
Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da wasu shugabannin jihohi 16, sun amince da sabbin matakan yaki da cutar corona a kasar, abin da ya sanya su kara tsawaita dokar kulle zuwa karshen wannan wata na Janairu.
Matakan sun hada da tsaurara tafiye-tafiye a kewayen akalla kilomita 15 ga mazauna yankunan da annobar ke da kamari a cikin su.
Wani matakin shi ne sake tsaurara hani a kan taron jama'a, inda haduwa ba za ta wuce ta mutum guda tsakanin mazauna mabambanta gidaje ba.
Dama dai a yanzu mutum biyar-biyar daga gidaje biyu na iya haduwa a lokaci guda.