1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Dambarwar kafa Hisbah mai zaman kanta

Nasir Salisu Zango
December 9, 2025

Kokarin kafa sabuwar Hisbah mai zaman kanta a Kano karkashin tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ta janyo cece-kuce a tsakanin masana fannin tsaro

https://p.dw.com/p/551pe
Ofishin hukumar Hisbah a Kano
Ofishin hukumar Hisbah a KanoHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Tun lokacin da tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya fara furucin kafa Hisbah mai zmana kanta a kano aka bude sabon shafin muhawara inda masana ke cewar tamkar girka gwamnati ne mai zaman kanta, sai dai tsagin tafiyar Ganduje sun yi burus sukar lamirin wannan yunkuri inda tuni suka fara rabon fom ga masu shaawar shiga.

Wannan lamari ya sake bude sabon shafin muhawara. Barista Amina Umar Hussein lauya ce a Kano ita ce shugabar kungiyar mata lauyoyi zalla ta FIDA a Kano, ta ce matukar ba majalisa aka kai hukumar aka yi mata doka ba to Ganduje ba shi da ikon kafa hukuma mai irin aikin Hisbah sai dai fa idan ya yi niyyar takalar fada ne

To sai dai a nasa bangaren babban jigo a tafiyar gidauniyar Ganduje Dr Muhammad Harun Ibni sina wanda ya yi shugabancin hukumar Hisbah zamanin mulkin Ganduje ya ce suna nan daram wajen wannan aniya tasu kuma tsarin su zai taimaka wa Hisbah ta Kano wajen ayyukanta

Barista Abba Hikima Fagge lauya mai fafutukat kare hakkin dan Adam ya ce idan tsari za a zo da shin a wa'azi da yi wa jama'a sulhu babu laifi amma matukar abin ya wuce haka akwai matsaloli.

Sai dai tsagin Ganduje sun ce sun yi nisa wajen raba fom din wannan tafiya, lamarin da masana ke cewar ayi hattara domin kauce wa rura wutar rikici a daidai lokacin da zaman lafiya ke samun tazgaro.