1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa ayyukan gona a kasar Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
February 19, 2026

Burkina Faso da Majalisar Dinkin Duniya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta samar da kuɗi don aiwatar da ayyukan ci gaban al'umma

https://p.dw.com/p/592V1
Aikin noma a Burkina Faso
Aikin noma a Burkina FasoHoto: DW

Sha'anin noma a  Burkina Faso yana samun kyakkyawan sakamako. A kakar 2025, yawan amfanin gona da aka samu ya kai tan miliyan bakwai, wanda ya karu da kashi 8% ciki dari  bisa ga alkaluman hukuma.

Domin ƙarfafa wannan ci gaba, an tsara shirye-shirye guda uku tare da tallafin Majalisar Dinkin Duniya, waɗanda suka kai sama da biliyan 850 na CFA, ko Dala biliyan daya da rabi na Amurka.

Wannan yunkurin shi ne na ganin Burkina Faso ta kara yin azama wajen ciyar da kanta da kuma samun wadatar abinci ba tare da yin dogaro da kasashen waje ba.

Karfafa Gwiwar manoma

Ci gaban aikin gona a Burkina Faso
Ci gaban aikin gona a Burkina FasoHoto: DW

Za a kara karfafa ayyukan gona inda matsalar tsaro ta tilasta wa mutane ficewa. Maurice Azonnankpo shi ne mukadashin shugaban kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya a Burkina Faso

"Ayyukan haɗin gwiwa da muka yi tun daga shekarar 2024 sun haifar da shirye-shirye guda uku da za su kawo sauyi a Burkina Faso. Kasar na nuna kuzarin girmama ikon mallakar Burkina Faso daga al'umma ta yadda za su tsaya da kafaffunsu, huldar mu da su mai kwari ce.'*

Yankin  Lptako na daga cikin yankunan da ke fuskantar kalubale na masu jihadi , wanda rashin tsaro ya shafa, ana buƙatar wannan tallafi inji Amadou Dicko, shugaban ƙungiyar manoman yankin.

Samar da kudi don tallafa wa manoma

Feshin maganin kwari a gona
Feshin maganin kwari a gonaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Ana iya yin amfani da wannan kuɗin don tallafa wa wannan al'umma ta yankin Liptako mai juriya wacce, duk da yanayin tsaro na hare-haren da ake kai musu, ta yanke shawarar ci gaba da gudanar da aikin gona don biyan buƙatunta."

Noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Burkina Faso, wanda sama da kashi 80 na al'ummar ke yi. Galibi suna noma Gero da Masara da Dawo da Gyada da kuma Kada. To amma hare-hare da ‘yan ta'adda suke kai wa yankin arewacin kasar ya sa al'ummar yankin da dama sun fice sun yi watsi da aikin gonar.