1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa huldar dangantaka tsakanin Nijar da Aljeriya

Salissou Boukari
January 27, 2026

Bayan tsamin dangantaka na tsawon lokaci tsakanin Nijar da Aljeriya da ma kasashen AES, Aljeriya ta sake dawowa a wannan karon da wata babbar tawaga domin dorawa daga inda aka tsaya kan huldarsu da Jamhuriyar Nijar

https://p.dw.com/p/57Z73
Kamfanin hakar ma'adanai a Nijar
Kamfanin hakar ma'adanai a NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Bangarorin biyu dai da suka hada da tawagar Ministan man fetur na kasar Aljeriya Mohammed Arkab, da na kasar Nijar sun tattauna batutuwan da za su kawo ci gaba ga kasashen biyu musamman a fannin man fetur, inda Aljeriya za ta yi aikin fitar da mai da iskar gas a yankin arewacin Nijar tare da hada hannu da kamfamni mai na SONATRACH na Alejeriya, da SONIDEP Nijar, musamman aikin bincike da kamfanin kasa ke gudanarwa a yankin Kafra, da ke arewacin Nijar inda ake da rijiyoyin mai da aka kiyasta samun ganga miliyan 250, wanda zai kara yawan man da Nijar ke hakowa a rana da ganga miliyan tasa’in 

Ministan mai na Aljeriya Malam Mohamed Arkab, ya baiyana aniyar kasarsa na aiki hannu da hannu da kasar Nijar ganin yadda suke da kwarewa ta shakaru da dama a wannan fanni. Da yake magana kan wannan batu Inoussa Dodo Hambal, shugaban kungiyar da ke fafutikar ganin arzikin karkashin kasa na Nijar ya amfanni yan Nijar, ya ce bunkasa tattalin arziki ba a saka siyasai a cikin shi illa ribar da kowa zai samu don ci gaban al’umominsu.

A baya dai kasashen AES musamman kasar Mali ta zargi Aljeriya da yin kafar ungulu a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda wanda ya sanya tsamin dangantaka a tsakaninsu. Sai dai ganin yadda tawagar Aljeriya ta iso Nijar da kuma tarbar da ta samu na nuni da cewa an samu cikakiyar fahimtar juna.