1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
CinikiKenya

Kenya tana neman karfafa dangantaka da Somaliya

Cai Nebe | Mouhamadou Awal Balarabe SB
February 26, 2026

Kenyan William Ruto na Kenya na neman karfafa dangantaka tsakanin kasarsa da kuma Somaliya amma bude iyaka na ha haifar da fargaba saboda mayakan Al-Shabab na ci gaba da kai hare-hare.

https://p.dw.com/p/59Syb
Shugaba William Ruto na Kenya
Shugaba William Ruto na KenyaHoto: Shisia Wasilwa/DW

Shugaban Kenya William Ruto na neman habaka harkokin cinikayya tsakanin kasarsa da makwabta na gabashin Afirka ciki har da Somaliya. Amma bude iyakokin da ya yi na haifar da fargaba a kan iyakokon kasashen biyu sakamakon barazanar hare-hare daga kungiyar Al-Shabab na Somaliya.

Kokarin kasar Somaliya na bude kofofinta ya kama hanyar zama wani abu na zahiri bayan da Shugaba William Ruto na Kenya ya sanar da sake bude iyakoki biyu a watan Afrilu. A hukumance dai, an rufe iyakokin kasar Kenya da Somaliya tun 2011, ko da yake makwabtan biyu yi yunkurin bude su a baya kafin yunkurin ya ci tura.

An jima da amincewa da sake bude iyaka

Wasu shugabannin Afirka
Wasu shugabannin AfirkaHoto: Ethiopian PM Office

A watan Mayun 2023 ne kasashen biyu suka amince da sake bude kan iyakarsu. Sai dai Kenya ta sauya shawarar watanni biyu bayan kisan fararen hula biyar da jami'an 'yan sanda takwas a kusa da kan iyaka a hare-haren da ake zargin Kungiyar Al-Shabab mai alaka da al-Qaeda da kaiwa. A gefe guda kuma, sassa biyu na takaddama a kan iyakar mai tsawon kilomita 680 game da wani yanki mai arzikin mai da iskar gas.

'Yan kasuwar kasar Somaliya sun yi maraba da bude kan iyakar kasarsu da Kenya. Ahmed Barre Diriye, wani shugaban al'umma a Beled Hawo da ke kan iyaka da Mandera ta Kenya yana matukar farin ciki da yiwuwar bude kan iyaka.

Shugaba William Ruto na Kenya
Shugaba William Ruto na KenyaHoto: Daniel Irungu/dpa/picture alliance

Dama dai a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Ruto ya ce bai kamata 'yan Kenya da ke garin Mandera su rabu da danginsu na Somaliya na tsawon lokaci saboda rufe iyakar Mandera ba.

Amma a cewar mai sharhi kan tattalin arziki na Somaliya Ahmed Khadar, akwai dalilai karfafa a fannin tattalin arziki da ke sa Somaliya da Kenya su kara kusantar juna.

Somaliya tana neman karfafa dangantaka da kasashen Afirka

Wannan matakin ya biyo bayan kokarin da gwamnatin Somaliya ke yi na kara samun hadin kan sauran kaasshen Afirka, da neman habaka ciniki da yawon bude ido a kasar da ke yankin kahon Afirka. Hasali ma dai, Somaliya ta fara ba da biza ta yanar gizo da biza a filin jirgin sama ga matafiya da suka iso.

Dakarun kasashen da ke aiki a Somaliya
Dakarun kasashen da ke aiki a SomaliyaHoto: Mahamud Hassan/AU UN IST Photo | CC0 1.0

Sannan a wannan wata na fabrairu, Somaliya ta shiga tsarin fasfo na bai daya na kungiyar raya arzikin gabashin Afirka  bayan ta zama memba a shekarar 2024 don habaka ciniki da saukake tafiye-tafiye ga 'yan kasar.

a daya hannun kuma, gwamnatin Mogadishu na tallata Somaliya a matsayin wani wuri mai muhimmanci na yawon bude ido. A  babban birnin kasar, wasu masu yawon bude ido na kasashen Yamma sun fara kashe kwarkwatar idanunsi a baraguzan gine-gine masu girma da ke kusa da bakin teku.