Kasashen duniya na martani kan harin Iran
March 1, 2026
A wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen Jamus da Faransa da Burtaniya suka fidda sun yi Allah wadai da hare-haren da Iran ke kaiwa wasu kasashen yankin, sun ce tilas ne Tehran ta kaurace wa hare-haren wuce gona da iri na soji.
Kasashen uku sun kuma bukaci a koma teburin tattaunawa. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi gargadin cewa duk wani tashin hankali dole ne kawo karshen shi.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce EU za ta ci gaba da jajircewa don kare tsaro da ma zaman lafiyar yankin, kuma yana da muhimmanci a tabbatar da tsaron nukiliya da kuma hana ayyukan da za su kara ta'azzara rikicin.
Firaministan Burtaniya Keir Stamer ya ce dole ne a kaucewa duk wani abu da zai iya rura wutar rikicin ga daukacin yankin.
Rasha ta bukaci dakatar da hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai wa cikin gaggawa, inda ta ce maslaha ta diplomasiyya ita ce kadai mafita.
Karin bayani:Tashin hankali na kara yin muni a Gabas ta Tsakiyya